Gajeren Ciwon Sukari

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gajeren Ciwon Sukari



Hoto: WHO International


Gabatarwa

Gajeren ciwon sukari, wato prediabetes, yanayi ne da sinadarin bilkodi yake yin yawa fiye da buƙata a cikin jini sannan kuma adadin ƙaruwar tasa bai kai a kira shi ciwon sukari nau’i na biyu ba (type 2 diabetes). Shi ne matakin farko na kaiwa ga duk wani nau’in ciwon sukari matuƙar dai ba a ɗauki mataki tun a kan kari ba. Kenan, da zarar sinadarin bilkodi ya haura yadda ake buƙata a cikin jini, to wannan yanayi ya zama gajeren ciwon sukari.

Wannan ciwo, ciwo ne da yake yi wa ɗan’adam kisan mummuƙe, kasantuwar mutum yakan kasance a cikinsa tsawon lokaci ba tare da ma ya san yana ɗauke da shi ba, har sai lokacin da ya fara lalata wasu muhimman sassan jiki da suka haɗa da ƙoda, idanuwa, da sauransu sannan a farga, wanda kuma, tuni an riga an shiga matakin ciwon sukari nau’i na biyu. Sai dai, duk da haka, canja yanayin rayuwa ta hanyar cin lafiyayyen abinci mai gina jiki yakan kawar da wannan matsala baki ɗaya.

Wani bincike da aka gudanar a Amurka ya tabbatar da cewa: “Kusan Amurkawa miliyan 88; wato kwatankwacin sama da mutum ɗaya a duk cikin mutane uku ne suke cikin wannan yanayi. Kuma kusan kashi 84 cikin ɗari (84%) na masu ɗauke da wannan yanayi basu san suna ciki ba”, Center for Disease Control and Prevention, (2020).

Abubuwan da Ke Haddasa Gajeren Ciwon Sukari

Rashin karɓar sinadarin insulin daga ƙwayoyin halittar jiki yadda ya dace; wato suna karɓa amma ba yadda ya dace ba, shi ne abin da ke sabbaba samun yawaitar sinadarin bilkodi a cikin jini. Kamar yadda Center for Disease Control and Prevention (2020), ta zayyana.

Alamomi

Babu wata alama da ke nuna an kamu da gajeren ciwon sukari. Amma masana (Center for Disease Control and Prevention, 2020; Mayo Clinic, 2020; Dansinger, 2019; Higuera da Huffman, 2018) sun zayyano abubuwan da ke ƙasa a matsayin ababen da ke kaiwa ga kamuwa da wannan cuta.

  • Nauyi maras misali.
  • Ƙugun namijin da kaurinsa ya haura 40 mace kuma 35.
  • Ƙiba maras misali musamman mai haɗe da tumbi.
  • Yawan cin jan nama.
  • Yawan shekarun da suka haura 45.
  • Rashin samun isasshen barci.
  • Gado; samun ɗaya daga cikin mahaifa, ƙanne ko yayye mai ɗauke da ciwon sukari mataki nau’i na biyu.
  • Rashin motsa jiki akai-akai.
  • Ƙabila da launin fata suma suna daga cikin abubuwan da ke zama sanadin kamuwa da wannan ciwo. Mutane irin Amurkawan asali, Latinawa (Latino) Afirkawa-Amurkawa (Africans-Americans), Indiyawa-Amurkawa (Indians-Americans), mutanten Tsibirin-Fasifik (Pacific Islanders) da Kuma wasu daga cikin Asiyawa-Amurkawa (Asians-Americans) duk suna cikin hatsarin kamuwa da wannan cuta.

Gwaji

Bisa dalilan da suka gabata, babu wata ingantacciyar hanya da za a iya gane ana tare da wannan yanayi na gajeren ciwon sukari da ya wuce gwajin kimiyya. Haƙiƙa zuwa asibiti domin gwada adadin sinadarin bilkodi, wanda aka fi sani da sukarin jini (blood sugar), ita ce hanya ɗaya sananniya da ake gane kamuwa ko akasin haka daga wannan larura.

Hanyoyi/Matakan Kariya

Wannan kuma albishir ne ga masu ɗauke da wannan cuta da ma waɗanda suke fuskantar barazanar kamuwa da ita cewa, ana warkewa tsaf tare kuma da kare kamuwa da ita. Ga hanyoyin da za a bi:

  • Motsa jiki na aƙalla minti 30 a kowace rana.
  • Rage nauyi.
  • Cin ingantaccen abinci mai gina jiki.
  • Daidaita adadin gudun jini (blood pressure) da kuma yawan maiƙo (cholesterol).
  • Yawan amfani da ‘ya’yan itatuwa da suka haɗa da lemon zaƙi,
  • Rage yawan zuƙar hayaƙin taba.
  • Rage yawan kwankwaɗar barasa, inda hali ma a daina, domin kuwa zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.

Manazarta:


Dansinger M. (2019). Prediabetes (Borderline Diabetes). An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.webmd.com/diabetes/what-is-prediabetes

Center for Disease Control and Prevention (2020). Prediabetes - Your Chance to Prevent Type 2 Diabetes. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.cdc.gov/diabetes/basics/prediabetes.html

Cherney K. (2019). The Right Diet for Prediabetes. An Ciro a shearer 2021 data shaken: https://www.healthline.com/health/diabetes/prediabetes-diet

Higuera V. da Huffman B. (2018).  What Is Prediabetes? An Ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.healthline.com/health/type-2-diabetes/what-is-prediabetes#symptoms

United Nnations (2021). World Diabetes Day. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.un.org/en/observances/diabetes-day

Mayo Clinic (2020). Prediabetes. 1998-2021 Mayo Foundation for Medical Education and Research (MFMER).  An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.mayoclinic.org/diseases-conditions/prediabetes/symptoms-causes/syc-20355278


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub